Manchester United Ta Sake Taya Danwasa Alderweireld!

Manchester United Ta Sake Taya Danwasa Alderweireld!

Manchester United ta sake taya dan wasan bayan Tottenham,mai shekara 29, Toby Alderweireld, in ji (Mirror).
Chelsea za ta biya fam miliyan 89 kan Jan Oblak na Atletico Madrid domin sayen golan Sloveniyar, mai shekara 25, inda zai maye gurbin mai tsaron gidan Belgium, mai shkeara 26, Thibaut Courtois, wanda ya shirya domin koma wa Real Madridkamar yaddaMundo Deportivo.ta bayyana.
A maimakon haka kuma, Chelsea za ta yi kokarin sayen golan Stokemai shekara 25, Jack Butland, idan Courtois ya tafi, a cewar (Sky Sports).
Chelsea tana nazari kan sayen Butland kan kudi fam miliyan 25, kamar yadda jaridar (Star)ta ruwaito.
Roma tana zawarcin dan wasan tsakiyarTottenham dan kasar Kenya, Victor Wanyama, mai shekara 27, kamar yadda jaridarLa Repubblica, ta bayyana.
Fulham ta son sayen dan wasan bayan Belgium, Dedryk Boyata, amma Celtic ba ta son sayar da shi, in ji jaridar (Mail).
Arsenal za ta iya sayar da dan wasan Ingila, mai shekara 27, Danny Welbeck, kamar yadda jaridar(Evening Standard) ta ruwaito.
Dan wasan tsakiyar Croatia, Luka Modric, mai shekara 32, yana tunanin barin Real Madriddomin kwadayin yarjejeniya mai maiko dagaInter Milanin ji(La Sexta - in Spanish).
Shugaban kungiyar Lyon Jean-Michel Aulas ya ce dan wasan bayan Barcelona,mai shekara 23, Yerry Mina yana son koma wa kulob din na Faransa, duk da cewa rahotanni na cewa dan wasan na kasar Colombia ya shirya domin komawa Evertonkamar yadda(Liverpool Echo)ta ce.
Manchester United na shirin zawarcin dan wasan Lazio Sergej Milinkovic-Savic, a cewar(Calciomercato).
Dan wasan Real Madrid Mateo Kovacic ya ki zuwa atisaye a wani yunkuri na take-takensa don barin kungiyar, in ji (Marca).
Burnleyta shirya sayen dan wasan Stoke Peter Crouch, kamar yadda jaridar (Sun) ta ruwaito.

Show Us Some Love By Sharing Our Articles