Ruwan Da Aka Sako Daga Kasar Kamaru Ya Hadasa Ambaliyar Ruwa A Adamawa Da Taraba

Ruwan Da Aka Sako Daga Kasar Kamaru Ya Hadasa Ambaliyar Ruwa A Adamawa Da Taraba

A ziyarar jaje da ya kaiwa wasu da ambaliyar ta shafa, gwamnan jihar Adamawa Senata Muhammadu Bindo Jibrilla, ya gargadi jama’a dake zaune a gabar kogin Binuwai, da kuma masu gina gidaje a hanyar ruwa da ayi taka tsantsan don gudun irin abin da ya auku.

A baya dai dubban jama’a sun sha rasa muhallansu ta sanadiyar sako ruwa na Ladgo da jamhuriyar Kamaru ke yi, Kuma hakan na faruwa ne saoda kunnen kashi da gargadin da hukumomi ke yi na mutane su daina gini kan madatsar ruwa.

Show Us Some Love By Sharing Our Articles