Marcelo Yana Son Komawa Juventuse Da Gaske!!

Marcelo Yana Son Komawa Juventuse Da Gaske!!

Dan wasan Real Madrid Marcelo yanzu haka dai yana can ya karkata tunaninsa wajen tafiya kungiyar da babban abokinsa Ronaldo ya koma wato Juventus domin su cigaba da buga wasa tare.

Dan bayan da yake buga gefe yana dai cikin shekarunsa na 13 a kungiyar ta Real Madrid ya kuma lashe gasar Laliga har 4 da kuma gasar zakarun Nahiyar Turai ta (Champions League) shi ma 4.

Amma sai dai bayan tafiyar abokin nasa Ronaldo zuwa Juventus dake buga wasa a Italiya a gasar Serie A ya na nazarin binsa.

Wata majiya ta El Confidencial ta rawaito cewa Marcelo da Ronaldo sun shaku sosai, ana sanya ran nan da watan Janairu mai zuwa zai matsa kaimi wajen ganin ya bi aminin nasa tunda an kamala cinikayyar wasanni ta bana yanzu.

Sai dai a kwanakin baya dan wasan ya bayyana cewa yana farin ciki da zama a kungiyar kuma bazai takurawa shugabannin kungiyar dole sai yabar kungiyar ba amma kuma yace komai yana iya kasancewa.

Show Us Some Love By Sharing Our Articles